30 Disamba 2019 - 09:15
Iran Da Kawayenta Za Su Iya Tabbatar Da Tsaro A Yankin Ba Tare Da Sojojin Kasashen Waje Ba.

Birgediya Janar Ibrahim Dehghani ya bayyana cewa kasar Iran da kawayenta za su iya kula da tsaron yankin ba tare da bukatar wasu sojojin kasashen waje ba, kuma ya fadi hakan ne a daidai lokacin da ake gudanar da atisayan hadin gwiwa tsakanin kasashen Iran Rasha da kuma kasar China a ruwan Oman da tekun India.

(ABNA24.com) Birgediya Janar Ibrahim Dehghani ya bayyana cewa kasar Iran da kawayenta za su iya kula da tsaron yankin ba tare da bukatar wasu sojojin kasashen waje ba, kuma ya fadi hakan ne a daidai lokacin da ake gudanar da atisayan hadin gwiwa tsakanin kasashen Iran Rasha da kuma kasar China a ruwan Oman da tekun India.

Atiyasan da aka gudanar da shi a wuri mai fadin mita murabba’in 17,000 ya hada da nuna sabbin dabarun yaki, da gwajin yadda za’a tunkari masu fashin jirgin ruwa a cikin teku da sauran dabarun yaki a cikin teku.

A nasa bangaren kwanadan dakarun ruwa na kasar Iran Rear Admiral Hossain Khanzadi ya bayyana cewa dole ne Amurka ta bar yankin nan, domin lokacin yin babakere da kan kane wuri da Amurka take yi, ya zo karshe don haka ya kamata ta fara tattara na ta ya na ta ta bar yankin.

Har il yau shi ma kwamandan hafsoshin sojin kasa na kasar Iran Rear Admiral Habibollah Sayyari da yake bayani ga manema labarai ya fadi cewa: Atisayin hadin guiwa zai kara kusanto da kasashen yankin , kuma yana nuna irin aniyar da bangarorin 3 suke da ita wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin ba tare da taimakon dakarun wata bakuwar kasa ba.



/129


/129